Bangaren siyasa da zamantakewa;masu niyar sabke aikin umra a bana daga birnin Islam abad fadar mulkin kasar Pakistan sun sabka a birnin Madina kuma wannan it ace tawaga ta farko a bana.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: masu niyar sabke aikin umra a bana daga birnin Islam abad fadar mulkin kasar Pakistan sun sabka a birnin Madina kuma wannan it ace tawaga ta farko a bana.Wannan shi ne karon farko da aka bawa kamfanin jigilar masu bulagoro dad a kamfanin PAA na kasar Pakistan ya dauki masu kokarin sabke umra daga wannan birni kai tsaye har zuwa birnin Madina na kasar Saudiya kuma dama ya taba kwasar masu umra daga garuruwan Multan da Karachi ta hanyar amfani da hanyar jiragen sama kai tsaye har zuwa birnin n amadina ma'ana ba tare da yada zango a wata kasa ko wani birni na kan hanya kafin isa birnin na Madina. Kafin haka dai da farko mahajjata da masu son sabke aikin umra suna sabka ne a birnin Jidda na Saudiyar kafin su isa birnin Madina nan amma wannan karon kai tsaye za su sabka a birnin Madina.
972303