IQNA

Sarkin Kasar Bahrain Ya Shiga Rudani Bayan da Ya Dauki matakin Kashe Masu Bore

20:08 - March 18, 2012
Lambar Labari: 2293629
Bangaren kasa da kasa, sarkin kasar Bahrain ya shiga rudani bayan day a dauki matakin yin kisan gilla kan fararen masu zanga-zanga maimakon sauraren kukansu da kuma warware komai ta hanyanr lumana kamar yadda masu boren suke yinsa ta hanyar lumana.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, sarkin kasar Bahrain ya shiga rudani bayan day a dauki matakin yin kisan gilla kan fararen masu zanga-zanga maimakon sauraren kukansu da kuma warware komai ta hanyanr lumana kamar yadda masu boren suke yinsa ta hanyar lumana, wanda kuma hakan ne kawai hanyar zaman lafiya akasar.
Yanzu haka dai al'ummar kasar Bahrain sun bukaci dakarun mamaya na kasar Saudiyya da su fice daga kasar, bayan da suka kwashe shekara guda suna taimakama masarautar kasar wajen murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana domin tabbatar da zalunci a kansu.
A jawabin da ya gabatar a gaban dubban daruruwan mutane da suka taru a kusa da birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, Sheikh Ali Salman shugaban jam'iyar Al-wifaq jam'iyyar adawar siyasa mafi girma a kasar, ya bayyana cewa da ya kamata ne Saudiyya ta zama mai shiga tsakani domin warware matsalar al'ummar Bahrain, maimakon ta zama daya daga cikin bangarorin rikicin biyu.
Malamin ya ce yin amfani da karfi da masarautar Bahrain ke yi kan fararen hula masu zanga-zangar lumana, tare da taimakon sojojin Saudiyya, babu abin da zai kara sai fusata jama'a da kuma kara musu kaimi wajen ci gaba da borensu, domin kuwa abin da mutanen kasar suke bukata shi ne, sarki ya ci gaba da sarautarsa, amma mutane ke da hakkin zaben 'yan majalisa da za su zabi fira ministan, maimakon sarki ya zabi 'yan majalisa da kansa kuma ya nada fira ministan da ya ga dama, ba tare da nuna banbanci tsakanin al'ummar kasar ba kamar yadda ake nuna musu.

973372


















captcha