IQNA

Malamin Wahabiyawan saudiyya Ya Bayar Da fatawar Kai hare-hare kan majami'oi

16:43 - March 19, 2012
Lambar Labari: 2293776
Bangaren kasa da kasa, wani daya daga cikin malaman wahabiyawan saudiyya ya bayar da wata daga aljihunsa da ke halasta kai hare-haren ta'addanci kan majami'oi da sunan jihadi a duk inda aka samu halin yin hakan a cikin yankin Jazirar larabawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran Al-nakhil na kasar Iraki cewa, daya daga cikin malaman wahabiyawan saudiyya ya bayar da wata daga aljihunsa da ke halasta kai hare-haren ta'addanci kan majami'oi da sunan jihadi a duk inda aka samu halin yin hakan a cikin yankin Jazirar larabawa daidai da mahangarsa da kuma akidar da yake bi.
Wanda ya bayar da wannan fatawa shi ne babban jagoran kwamitin mamalami masu bayar da fatawa ga gwamnatin wahabiyawan Saudiyya da ake kira Abdulaziz Bin Abdulalh Ali-sheikh, wanda kuma shi ne matayin babban mamalin wahabiyawan saudiyya da ake komawa zuwa gare shi baki dayan kasar daga bangaren gwamnati.
Abdulaziz Bin Abdulalh daya daga cikin malaman wahabiyawan saudiyya ya bayar da fatawar ne daga aljihunsa da ke halasta kai hare-haren ta'addanci kan majami'oi da sunan jihadi a duk inda aka samu halin yin hakan a cikin yankin Jazirar larabawa, domin kara durmiya al'umma cikin wani riki, ta yadda za a manta da makircin da ake kitsawa al'ummomin duniya.
973779
captcha