Bangaren kasa da kasa, an sanar da ranar juma’ar da ta gabata amatsayin ranar kasa ta kur’ani mai tsarki a kasar Tunisia domin mayar da martani kan cin zarafi da keta alfarmar kur’ani da wani dan kasar ya yi a kawanakin baya da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-bashair cewa, an sanar da ranar juma’ar da ta gabata amatsayin ranar kasa ta kur’ani mai tsarki a kasar Tunisia domin mayar da martani kan cin zarafi da keta alfarmar kur’ani da wani dan kasar ya yi a kawanakin baya da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki wan da kasashen yammacin turai suka fakewa da shi domin keta alfarmar kur’ani da tozarta musulmi da musulunci.
Ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Tunisia ce ta sanar da hakan, wanda kuma zai ci gab aa kowace shekara, kasantuwar canjin da aka samu a kasar ba zai bayar da damar ci gaba da cin zarafin addinin muslunci kamar gwamnatin da ta gabata ba, wadda ta shara da kare manufofin kasashen yammacin turai.
Sanar da ranar juma’ar da ta gabata a matsayin ranar kasa ta kur’ani mai tsarki a kasar Tunisia domin mayar da martani kan cin zarafi da keta alfarmar kur’ani da wani dan kasar ya yi a kawanakin baya da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki, hakan wani gagarumin ci gaba da al’ummar kasar ta samu domin tabbatar da ‘yancinta.
974725