Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar goda da kum goma sha daya ga watan Farvardin na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Astana fadar mulkin wannan kasa aka shira gudanar da taron kasa da kasa ka addinai.A ranar bakwai ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wata ganawa da ImanAli Tash Muhammad Uf magajin garin Astana yayi da Rawul Ainul Dine babban muftin kasar kuma shugaban ofishin cibiyar kula da harkokin da suka shafi musulmin Rasha da ke zaune a birnin masko fadar mulkin kasar Rasha ya bada labarin gudanar da taron malaman addinai da za su tattaunawa lamura da suka shafi addini da kuma yadda za a kara kusanci da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai musamman magance rikice rikice da sabani na addini a tsakaninsu .Tuni masu lura da harkokin addinai a duniya suka bayyana gamsuwa da farin cikinsu kan manufar wannan taro da cewa ko shakka babu taron zai taimaka da kara kusanci a tsakanin mabiya addinai a kasashe daban daban na duniya.
975682