Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro domin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya ddinin muslunci da kuma mabiya addinin kiristanci da ma sauran addinai a birnin London na kasar Birtaniya tare da halartar malamai da masana daga sassa na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar ISESCO cewa, za a gudanar da wani zaman taro domin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya ddinin muslunci da kuma mabiya addinin kiristanci da ma sauran addinai a birnin London na kasar Birtaniya tare da halartar malamai da masana daga sassa na kasar da ma wasu kasashen ketare.
Wannan zaman taro yana daya daga cikin muhimamn taruka da kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu na muslunci ke shirin shiryawa abirnin na London, kuma ya samu karbuwa daga mutane da dama da aka aike musu da goron gayyatar halartar taron, musamman ma masana da malaman addinin muslunci na kasar da kuma wasu kasashen musulmi da na larabawa.
Gudanar da wani zaman taro domin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya ddinin muslunci da kuma mabiya addinin kiristanci da ma sauran addinai a birnin London na kasar Birtaniya tare da halartar malamai da masana daga sassa na kasar da ma wasu kasashen turai da suke makwaftaka da ita.
975896