IQNA

Mjasu Bore A Kasar Bahrain Sun Yi Allawadai Da Taron Kasashen Larabawa

22:19 - March 29, 2012
Lambar Labari: 2295725
Bangaren kasa da kasa, masu neman sauyi a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da taron da shugabannin kasashen larabawa suka gudanar a kasar Iraki saboda yadda zaman taron ya kawar da idonsa kan abin da yake faruwa a kasar na cin zarafin fararen hula masu zanga-zangar lumana.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wifaq cewa, masu neman sauyi a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da taron da shugabannin kasashen larabawa suka gudanar a kasar Iraki saboda yadda zaman taron ya kawar da idonsa kan abin da yake faruwa a kasar na cin zarafin fararen hula masu zanga-zangar lumana a fadin kasar ta Bahrain.
Gungun 14 ga watan Fabrairu da ke jagorantar boren neman sauyi a Bahrain, wanda dukkanin bangarori na kasa da kasa suka tabbatar da cewa sama da kashi tamanin cikin dari ne suke gudanar da wannan bore, gungun ya fitar da wani bayani da ya yi kakakusar suka a cikinsa, dangane da yadda wadannan kasashen suke nuna banbanci tsakanin al’ummomin larabawa.
Masu neman sauyi a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da taron da shugabannin kasashen larabawa suka gudanar a kasar Iraki saboda yadda zaman taron ya kawar da idonsa kan abin da yake faruwa a kasar na cin zarafin fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman hakkokinsu da aka haramta musu.
975924
captcha