Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Iraki ya goyi bayan kafa kasar palastinu mai cin ‘yancin gishin kanta da kuma babban birnin Qods mai alfarma duk kuwa da irin matakan matsin lamabar da yahudawan sahyuni da A,urka suke dauka kan al’ummar yankin kurdawa domin kada su saka kansu cikin rikicin larabawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, shugaban kasar Iraki ya goyi bayan kafa kasar palastinu mai cin ‘yancin gishin kanta da kuma babban birnin Qods mai alfarma duk kuwa da irin matakan matsin lamabar da yahudawan sahyuni da A,urka suke dauka kan al’ummar yankin kurdawa domin kada su saka kansu cikin rikicin larabawa da haramtacciyar kasar Isra’ila.
A nasa bangaren pira ministan yankin gaza a Palastinu Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, yankin gabas ta tsakiya ya zama wani wurin buga misali da gwagwarmayar neman ‘yanci da fita daga karshin mulkin zalunci da kama karyana azzaluman shugabanni da sarakuna.
Haniyya ya byayana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga al’ummar kasar Tunisia a ziyarar da yake gudanarwa a wasui daga cikin kasashen yankin da suka hada Masar da kuma Suda gami da Turkiya, inda yake jadda matsayin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas wajen ci gaba da yin gwagwarmaya domin samun ‘yancin al’ummar yankin.
Pira ministan yankin gaza a Palastinu Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, yankin gabas ta tsakiya ya zama wani wurin buga misali da gwagwarmayar neman ‘yanci da fita daga karshin mulkin zalunci da kama karya azzaluman shugabanninsu da suke azurta kansu da dukiyoyin da al’ummar kasar suke da su.
976390