Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: gwamnatin kasar faransa ta fitar da wani hukumci da a ciki take cewa: ta haramta shigar wasu manyan malaman musulunci hudi shiga kasarta domin halartar taron shekara shekara da musulman kasar suka saba gudanarwa.majiyar labarai ta people daily cewa: a daidai lokacin da bai wuce yan kwanaki bad a shugaban kasar faransa a cikin jawabinsa day a gabatar a lokacin yakin neman zabe day a kan kama a fadin kasar ya bayyana rashin jindadinsa da damuwarsa kan bulaguron da Yusuf Kardawi shugaban kungiyar malamai na duniyar musulmi zai yi a kasar sai gashi ma'aikatar harkokin wajan kasar ta fitar da wata sanarwa ta hana shigar wasu malamai uku na daban cikin hudu a cikin kasar ta faransa. A cikin wannan sanarwa da ministan harkokin wajan faransa alan Jippe da ministan cikin gida Klod Guyan suka sanya wa hannu suna bayyana cewa mun lura ne da bukatar shugaban kasa da damuwar day a nuna don haka muka dauki matakin hana wadannan malaman musulmi shiga kasar ta Faransa domin halartar wannan taro na shekara shekara na musulmin kasar. Malaman da aka hana shiga kasar ta Faransa sun hada da Akrama Sabri shugaban babban tawagar musulmin kudus kuma limamin Masallacin Kudus da kuma Sheik Mahmud Almisri wani mashahurin malamin addini a kasar masar da kuma Safwat Alhijazi shimna malami a kasar Masar kuma baban sakataren Darul Ansar da ke kula da harkokin kur'ani a kasar ta Masar sai kuma wani malami daga kasar Saudiya wadanda aka hana masu izinin shiga kasar ta Faransa.
976363