Bangaren kasa da kasa: a shekara ta dubu biyu da shida miladiyabayan nasarar da kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi ta samu a hari da mamaye da gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila ta kawo wa kasar labanon an samu karuwa masoya da masu kaunar Said Hasan nasrullahi babban sakataran kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi kuma wannan wata babbar nasara ce da falala a cikin harkokin siyasa na rayuwar said Hasan Nasrullahi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a shekara ta dubu biyu da shida miladiyabayan nasarar da kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullahi ta samu a hari da mamaye da gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila ta kawo wa kasar labanon an samu karuwa masoya da masu kaunar Said Hasan nasrullahi babban sakataran kungiyar gwagwarmaya ta hizbullahi kuma wannan wata babbar nasara ce da falala a cikin harkokin siyasa na rayuwar said Hasan Nasrullahi.Malik Sakur masani adabin larabci kuma fitaccen mai wake kuma maba a hadin kungiyar marubuta na larabawa a wata tattaunawa day a yi da kamfanin dillancin labarai na Ikna da kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; a shekara ta dubu biyu da shida milladiya bayan nasarar da kungiyar Hizbullahi ta samu kan gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila ya kara farin jinni da soyayya da kaunar Said Hasan Nasrullahi a tsakanin al'umma kuma a kasar Masar kawai an sanyawa yaran dari bakwai da aka Haifa sunansa kuma wannan na nuni da yadda yake samun karbuwa da farin jinni a tsakanin al'umma kuma haka farin jinisa ke karuwa a tsakanin al'ummomi daban daban na duniya musamman a kasashen larabawa da na yankin gabsar ta tsakiya.
972335