IQNA

Dangantaka Tsakanin Tunisia Da Isra’ila Ba Za Ta Koma Kamar Da Ba

16:12 - April 02, 2012
Lambar Labari: 2296619
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar masu kishin islama ta nahda a Tunisia ya bayyan acewa dangantaka tsakanin kasar da kuma haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta taba komawa kamar yadda take a da ba saboda canjin da aka samu a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo cewa, shugaban kungiyar masu kishin islama ta nahda a Tunisia ya bayyan acewa dangantaka tsakanin kasar da kuma haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta taba komawa kamar yadda take a da ba saboda canjin da aka samu a kasar da ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya mai dasawa da gwamnatin yahudawa.
A nata bangaren gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta maida martani kan tsai da dan takarar shugaban kasa da kungiyar 'yan uwa musulmi ta Ihwanul-Muslimin da ke kasar Masar ta yi, mataimakin fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila Mushe Ya'alun ya yi furuci da cewa; wanzuwar sulhu tsakanin kasar Masar da haramtacciyar kasar Isra'ila lamari ne da zai amfani dukkanin bangarorin biyu, kuma kare yarjejeniyar sulhun da ke tsakanin kasashen biyu hakki ne da ke kan duk wanda ya dare kan karagar shugabancin kasar.
Ya'alun ya kara da cewar kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasar Masar da Amurka zata ci gaba da gudana ce kawai matukar kasar Masar ta kare yarjejeniyar sulhun da ke tsakaninta da haramtacciyar kasar Isra'ila, ita dai kungiyar 'yan uwa musulmi ta Ihwan da ke kasar Masar ta tsai da Khairat Assha'dir ne a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa da za a gudanar a Masar a watan Mayu mai zuwa a nan gaba.
977042


captcha