IQNA

An Shiga Mataki Na Karshe A gasar Kur’ani Da Ake Yi A kasar Oman

16:12 - April 02, 2012
Lambar Labari: 2296620
Bangaren kasa da kasa, an shiga mataki na karshe a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Maskat fadar mulkin kasar Oman daya daga cikin kasashen musulmi da ke yankin tekun fasha.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ONA News cewa, yanzu haka dai an shiga mataki na karshe a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Maskat fadar mulkin kasar Oman daya daga cikin kasashen musulmi da ke yankin tekun fasha, da ke taka gagarumar rawa ta fuskar yada koyarwar kur’ani a tsaknain al’ummar kasar.
Wannan gasa dai tana samun halartar dalibai da makaranta gami da mahardata kimanin 285 daga sassa daban-daban na kasar, inda suke karawa da juna, kuma daga karshe za a fitar da sunayen wadanda suka lashe gasar a dukaknin bangarorin da aka gudanar da ita, inda za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.
Bayanin ya ci gaba da cewa an shiga mataki na karshe ne a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Maskat fadar mulkin kasar ta Oman, bayan wuce sauran matakai da ake bi a lokacin gudanar da irin wannan gasa a sauran kasashe, inda yanzu ne za a gudanar da bita ta sauran bangarorin da suka rage a matsayin mataki na karshen gasar baki daya.
977144


captcha