Bangaren kasa da kasa, majalisar dokokin kasar Turkiya ta amince da wani daftaron doka da ke bayar da damarr koyar da karatun kur’ani mai tsarki da tarihin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a makarantun gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa nayar gizo na mobashernews cewa, majalisar dokokin kasar Turkiya ta amince da wani daftaron doka da ke bayar da damarr koyar da karatun kur’ani mai tsarki da tarihin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a makarantun gwamnatin kasar wanda hakan ya kasance cikin abubuwanm da aka haramta.
Kasar Turkiya dai na daga cikin kasashen musulmi da suka yi nisa da koyarwar addinin muslunci, sakamakon tasirin mulkin raba addini da siyasa da kasar ta jima tana tafiya a kansa, duk kuwa da dan sauyin da aka samu a cikin harkokin siyasar kasar bayan da jam’iyar masu raya kishin addini ta karbi mulki akasar saboda abin da ta nuna ma mutane na cewa, za ta kamata addini a cikin da adalci, duk kuwa da cewa har yanzu muatnen kasar suna kokawa kan rashin cika wannan alkawali.
Amincewar da majalisar dokokin kasar Turkiya ta yi da wannan daftarin doka da ke bayar da damar koyar da karatun kur’ani mai tsarki da tarihin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a makarantun gwamnati ci gaba ne a cikin harkokin mulki, amma kuma hakan ba zai rasa nasaba da matsin lambar da mahukuntan kasar suke fuskanta ba, saboda matsaloli da dama da suke jawo raguwar farin jininsu a tsakanin al’ummar Tukiya.
977063