Bangaren al'adu da fasaha : A karon farko a jamhuriyar musulunci ta afganistan an buga da watsa wata mujalla ta addinin musulunci mai sunan mata musulmi kuma an fitar da ita a wannan mako ne da zumma da burin fito da martaba da matsayin mata musulmi a wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: A karon farko a jamhuriyar musulunci ta afganistan an buga da watsa wata mujalla ta addinin musulunci mai sunan mata musulmi kuma an fitar da ita a wannan mako ne da zumma da burin fito da martaba da matsayin mata musulmi a wannan kasa.Wannan mujalla ta kumshi abubuwa da dama da suka shafi rayuwar mata musulmi a wannan kasa ta jamhuriyar musulunci ta Afganistan kamar lamarin day a shafi ilimi al'adu zamantakewar mata a tsakaninsu da sauran takwarorinsu na kasar kuma wannan mujalla wata dama da hanya ce da matan za su bayyana matsayinsu da matsalolinsu da kuma taka rawar ganin kamar sauran takwarorinsu maza a wannan kasa kuma haka wani babban kalubale ne da makami ga matan illa iyaka ya rage nasu su bayyana matsayinsu da hakkinsu a bangarori daban daban na rayuwa.
976017