Bangaren ilimi da nazari: a ranar sha biyu ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Lakhuno da ke lardin Otarparadesh na kasar Indiya aka gudanar da taron karawa juna sani kan wajibci da muhimmancin samin malamai masu yin nazari da fitar da fatawa kan harkokin addini da kuma na zamantakewar al'umma da kuma muhimnaci da wajibcin bin malamai .
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar sha biyu ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Lakhuno da ke lardin Otarparadesh na kasar Indiya aka gudanar da taron karawa juna sani kan wajibci da muhimmancin samin malamai masu yin nazari da fitar da fatawa kan harkokin addini da kuma na zamantakewar al'umma da kuma muhimnaci da wajibcin bin malamai .A wajan wanna taron karawa juna sani an samu halartar malamai na addini kamar su said NizamulDine daga garin Haidar Abad da Ali Ahmad daga jidda da said Sulaiman Huseini daga garin Lakhuno wadanda suka yi nazari da bincike kan muhimman abubuwa da suka shafi addini da fikihu da bukatun dalibai na addini a wannan kasa.
977028