Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ma'a cewa, an fitar da wani bayani a Gaza da ke yin Allahwadai da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi yankin Janin da ke cikin yankin Palastinu wanda ahakan yake nuni da cewa masu adawa da musulunci ba su taba daga kafa kan irin wadannan ayyuka ban a tozarta addinin muslunci, a cikin kasashen turai ko na musiulmi, kamar yadda ke faruwa yanzu a Masar da kuma palastinu.
A wani labarin kuma a yayin da lokaci ya ke karatowa don komawa teburin shawar tsakanin Iran da gungun kasashe shida wato biyar masu kujerun dindindin a kwamitin tsaro gami da kasar Jamus, sakarariyar harkokin wajen kasar Amurka Hillary Clinton ta sake nanata kalaman shugaban kasar Amurka Barak Obama inda ya ce, "kofar diplomasiya tare da kasar ba zata ci gaba da kasancewa a bude har abada ba.
A zantawarta da ta yi da jaridar The Guardian ta kasar Ingila Clinton ta ce manufar Amurka dangane da wadannan shawarwari da Iran dai shi ne taimakawa wajen kawar da abinda ta kira damuwar kasashen duniya kan shirin nukiliyar Iran. Tare da maimaita irin wannan zargi maras tushe da kasashen Yamma suke yi na cewa da akwai abin damuwa dangance da ayyukan nukiliyar kasar Iran, Clinton ta kuma bayyana shakkunta a kan samun nasarar shawarwari da kasar Iran din tana mai cewa akwai sakamako takamaimai da Amurka take so a samu a shawarwarin.
Abinda sakatariyar harkokin wajen Amurka take fadi, wato kokarin samun ayyanannen sakamako daga zaman da za a yi da Iran, yana nufin cewa dai bata sake zani ba, kasar Amurka tana nan kan manufarta da ta saba hankali na cewa sai ta tilasta wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bar gudanar da ayyukan nukiliya na zaman lafiya, kuma tun farko ma Amurka ta san matsayar Iran dangane wannan batu.
976851