Bangaren kasa da kasa; kungiyar hadin kan musulmi ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da babbar murya kan matakin da gwamnatin Faransa karkashin umarnin shugabanta Sarkozi ya dauka na hana wasu masana da manazarta da kuma fitattun malamai shiga kasar ta Faransa domin halartar taron shekara shekara da musulmin faransa suka saba gudanarwa duk shekara.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kungiyar hadin kan musulmi ta fitar da wani bayani da a cikinsa take yin Allah wadai da babbar murya kan matakin da gwamnatin Faransa karkashin umarnin shugabanta Sarkozi ya dauka na hana wasu masana da manazarta da kuma fitattun malamai shiga kasar ta Faransa domin halartar taron shekara shekara da musulmin faransa suka saba gudanarwa duk shekara.An nakalto daga majiyar labarai ta uoif –online cewa: kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi allah wadai da babbar murya da matakin hadin guiwa da ma'aikatar harkokin wajan kasar Faransa tare da takwararta ma'aikatar cikin gidan Faransa ta dauka na hana izinin shiga kasar ta faransa domin halartar taron shekara shekara da musulmin kasar suka shirya a bana da cewa wannan mataki ne na siyasa da kuma ta danganta shi da harin da kungiyar dan takarar neman shugabancinfaransa Shugaba Nikola Sarkozy ke dauka na sa kafar wando guda da musulmin kasar da kuma daukan duk wani matakin takurawa musulmi da kungiyoyin musulmi a wannan kasar musamman idan aka yi la'akari da abubuwa da ke wakana a yanzu a wanann kasar.
9777726