Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; jam'iyar yan shi'a ta Gadir a kasar masar sun bayyana matsayinsu na goyan bayan dan takarar neman shugabancin kasa karkashin inuwar kungiyar Ikwanun Muslim a zaben shugabancin kasar mai zuwa. An nakalto daga majiyar jaridar Alyaum Sabi' da ake bugawa a kasar Masar cewa; jam'iyar mabiya darikar shi'a ta Gadir a kasar ta Masar sun nuna goyan bayansu dari bias dari ga Kheirat Alshatir dan takarar neman shugabancin kasar Masar a zabe mai zuwa karkashin inuwar kungiyar Ikwanul Muslim kuma jam'iyar ta yan shi'a t ace za ta taimakawa Alshatir a wannan zabe da ganin ya kai ga nasarar lashe wannan zabe na shugabancin kasar ta Masar da za a yi a nan gaba. Muhamamd Aldarini daya daga cikin mambobin farko na wannan jam'iya ta gadir ya bayyana cewa: sun dauki wannan mataki ne Shadir da kungiyar ikwanul Muslim ta dauka na bin diddigi da kawo karshen mabannata da barayi da masu aikin liken asiri a cikin kasar ta Masar.Kheirat Shatir mataimakin babban sakataren kungiyar Ikwanul Muslim yshi ne kungiyar ta tsayar a matsayin dan takararta a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a cikin wannan shekara ta dubu biyu da goma sha biyu da muke ciki.
977622