IQNA

Wasu Gwamnatocin Kasashen Larabawa Na Da Hannu Wajen Killace Gaza

18:27 - April 04, 2012
Lambar Labari: 2298105
Bangaren kasa da kasa, fira ministan Hamas a yankin Gaza ya bayyana cewa wasu daga cikin kasashen larabawa suna da hannu kai tsaye a cikin killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi tsawon shekaru.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-dastur ta kasar Jordan cewa, Isma’ila Haniyya fira ministan Hamas a yankin Gaza ya bayyana cewa wasu daga cikin kasashen larabawa suna da hannu kai tsaye a cikin killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi tsawon shekaru shida a jere.
A lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban dubban mutanen da suka taru a wata makabarta a Gaza, Isma’il Haniyya ya bayyana cewa abin ban takaici ne yadda wasu daga cikin kasashen larabawa suka zama da su ne ake hada baki tare da haramtacciyar kasar Isra’ila wajen yin kisan gilla kan al’ummar yankin Gaza, ba tare da lamiri na muslunci ko larabci ba, balanta lamiri na ‘yan adamtaka.
Isma’i Haniyya fira ministan Hamas a yankin Gaza ya bayyana cewa wasu daga cikin kasashen larabawa suna da hannu kai tsaye a cikin killace yankin zirin Gaza da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi tsawon shekaru aru-aru da suka gabata, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar dubban fararen hula, da suka hada da mata da kanan yara.
977461

captcha