Bangaren kasa da kasa: domin nuna adawa kan kisan gillar da aka yi wa wata mata musulma yar kasar Iraki mai suna Shima da wasu da ba a san ko suwa ne ba suka yi saboda kawai tana sanye da hijabin da addinin da ta yi imani da shi ya umurta don haka mata sama da miliyon daya wadanda ba musulmai bay an Amerika a cikin Face book sun sanya dan kwali a kansu.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; domin nuna adawa kan kisan gillar da aka yi wa wata mata musulma yar kasar Iraki mai suna Shima da wasu da ba a san ko suwa ne ba suka yi saboda kawai tana sanye da hijabin da addinin da ta yi imani da shi ya umurta don haka mata sama da miliyon daya wadanda ba musulmai bay an Amerika a cikin Face book sun sanya dan kwali a kansu.An nakalto daga jaridar Huffington Post cewa; mata sama da miliyon daya ne da ke cikin shafin nan na faceBook suka sanya hijabi wato dan kwali kuma wadannan mata Amerikawa ne kuma sun yi hakan ne domin nuna bakin ciki da adwa da kisan gilla da wasu yan ta'adda dab a a san ko suwa ne ba suka yi wa Shaima wata yar kasar Iraki don tana sanye da hijabin musulunci. Wannan zanga zanga da jerin gwano da matan Amerika suka yi ta hanyar shafin face book wani babban lamari ne da ke nuni da yadda duk wani mai lamiri a duniya musulmi ko wanda ba musulmi ba ke yaki da adawa da ayyukan ta'addanci da kisan gilla kan wanda bai san hawa balantana sabka ba. A ranar biyu ga watan farvardin ne na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka ga gawar Shaima yar shekaru talatin da biyu a duniya kuma tana da yaya biyar kuma an gano gawarta ne a gidanta a garin Alkajun na kaliforniya a Amerika kuma an azabtar da ita kafin a kasha tan kuma ta rubuta wasika cewa yan ta'adda ku koma kasarku.
978592