IQNA

Akwai Loje Cikin Nadi A Gudun Hijirar Siyasa Da Aka Bawa Hashimi

17:23 - April 05, 2012
Lambar Labari: 2298371
Bangaren kasa da kasa; Darik Hashimi wanda yake cikin jerin sunayan d Alirakiya kuma wanda ake zargi da ayyukan ta'addanci da kokarin kasha Nuri Almaliki firaministan Iraki bayan dambarwa da kce nacen siyasa mai sarkakiya ya bar yankin cin gashin kai na gurdawa zuwa kasar Katar tare da wucewa zuwa kasar Saudiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Darik Hashimi wanda yake cikin jerin sunayan d Alirakiya kuma wanda ake zargi da ayyukan ta'addanci da kokarin kasha Nuri Almaliki firaministan Iraki bayan dambarwa da kce nacen siyasa mai sarkakiya ya bar yankin cin gashin kai na gurdawa zuwa kasar Katar tare da wucewa zuwa kasar Saudiya.Mataimakin shugaban kasar Iraki da ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci ya tsere zuwa kasar Saudiyya.
Daya daga cikin makusantan mataimakin shugaban kasar Iraki Tarik Hashimi a yau laraba ya bayyana cewa; Mataimakin shugaban kasar ta Iraki Tarik Hashimi ya isa kasar Saudiyya daga kasar Qatar.

Tarik Hashimi dai ya tsere zuwa yankin Kurdawa da ke kudancin kasar Iraki ne bayan da kotu a birnin Bagadaza ta fitar da warantin kamoshi kan zargin hannu a shirya kai hare haren ta'addanci a kasar, sannan a ranar lahadin da ta gabata ya tsere zuwa birnin Doha na kasar Qatar, bayan da ya samu gayyata ta musamman daga sarkin kasar Sheikh Hammad bin Khalifa Ali-Sani, sai kuma a yau aka samu labarin isarsa kasar Saudiyya.

Zargin Tarik Hashimi da hannu a ayyukan ta'addanci dai ya zo ne bayan samun wasu kwararan dalilai da suke tabbatar da hannunsa a shirya kai hare haren ta'addanci har fiye da 150 gami da shaidar da masu tsaronsa na musamman suka bayar bayan da aka kame su da hannu dumu-dumu a kai hare haren ta'addanci a kasar ta Iraki.



978593
captcha