IQNA

A Karon farko A Brazil An Nuna Kayan Sanyawa Na musulmi

Bangaren al'adu da fasaha; an baje kolin kayan mata na musulmi musamman da suka kumshi hijabi da kayan dake suturta jikin mace da cibiyar musulunci a Brazil a garin Sanopanolo ta baje a karon farko.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an baje kolin kayan mata na musulmi musamman da suka kumshi hijabi da kayan dake suturta jikin mace da cibiyar musulunci a Brazil a garin Sanopanolo ta baje a karon farko. Baje kolin kayan musulunci da kuma suke suturta jikin mace domin kuwa sun hada da hijabi da wannan cibiya ta yi ko ba komi na nuni da yadda addinin musulunci da al'adun musulunci yake ci gaba da ratsawa da kuma samin karbuwa a wannan kasa ta brazil da ke yankin latine na Amerika kuma wannan ya kara tabbatar da rahotonnin da ke bayyana cewa musulunci na kara samin karuwa da karbuwa a tsakanin al'ummomi daban daban na duniya day a hada nahiyoyin Turai da na amerika.
978581