IQNA

Limamin Juma’a A Bahrain Ya Ce Mahukuntan Kasar Su Ne Manyan makaryata

23:41 - April 08, 2012
Lambar Labari: 2300437
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci kuma limamin kasar Bahrain ya bayyana cewa mahukuntan kasar manyan makaryatane domin kuwa suna bayyana ma duniya wani abu daban sabanin abin da suke aikatawa na ta’addanci da zalunci kan al’ummar kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakato daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, Sheikh Isa Kasim babban malamin addinin muslunci kuma limamin kasar Bahrain ya bayyana cewa mahukuntan kasar manyan makaryatane domin kuwa suna bayyana ma duniya wani abu daban sabanin abin da suke aikatawa na ta’addanci da zalunci kan al’ummar kasar marassa kriya.
Daya daga cikin membobin kungiyar 'yan jaridar kasashen larabawa a Amurka ya zargi wasu kasashen larabawa da na yammaci da kaddamar da gagarumin yakin jirkitar hakikanin abin da ke faruwa a kasar Siriya don cimma manufar da suka sa a gaba kan kasar.
A wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin din Press mai watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran cikin harshen turanci, Rafik Lutf memba a kungiyar 'yan jaridar kasashen larabawa a Amurkan ya ce tashar talabijin din nan ta Amurka da Al-Jazeera ta kasar Qatar da sauran wasu tashohin kasashen larabawan su ne kan gaba wajen jirkita hakikanin abin da ke gudana a kasar Siriya da kuma zargin gwamnati da kashe fararen hula alhali hakan aiki ne na 'yan ta'addan da suke samun makamai daga wajen wadannan kasashen.
Har ila yau dan jaridar ya zargi tashohin da Aljazeera da watsa hotuna da faifai na bidiyo na karya kan abubuwan da ke faruwa a kasar Siriya. An jima dai ana zargin wadannan tashoshi musamman Al-Jazeera da shirya irin wadannan karararrki kan wasu kasashen larabawa da nufin cimma manufofin Amurka da na yahudawan sahyoniya.
979707





captcha