IQNA

Watsa Bayanai Na Keta Alfarmar Kur’ani Ba Shi Ne Ma’anar Fdain Albarkacin Baki Ba

23:37 - April 09, 2012
Lambar Labari: 2301298
Bangaren kasa da kasa, ofishin shugaban kasar Tunisia ya fitar da wani bayani da acikinsa yake bayyana cewa yin wasu kalamai na keta alfarmar addinin muslunci ba shi ne ma’anar fadin albarkacin baki ba kamar yadda wasu suka dauka kuma suke amfani da wannan damar domin cin zarafin musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na businessnews cewa, ofishin shugaban kasar Tunisia ya fitar da wani bayani da acikinsa yake bayyana cewa yin wasu kalamai na keta alfarmar addinin muslunci ba shi ne ma’anar fadin albarkacin baki ba kamar yadda wasu suka dauka kuma suke amfani da wannan damar domin cin zarafin musulmi a cikin kasar da ma wajenta.
Baynain ya ce dole kowa ya girmama addinin kowane bangare a cikin dokokin kasar Tunisia, musulmi ba shi da hakkin ya ci zarafin wani saboda shi ba musulmi ba ne, kamar yadda wani wanda ba musulmi ba ba shi da ahhaki ko hurumin cin zarafin muslmi, haka nan kuma ko da musulmin ne ba shi da hakkin ya yi kalaman batunci kan akidar musulmci saboda wasu ra’yoyi nasa, yin hakan ya saba ma kundin tsarin mulki.
A cikin wannan makon ne ofishin shugaban kasar Tunisia ya fitar da wani bayani da acikinsa yake bayyana cewa yin wasu kalamai na keta alfarmar addinin muslunci ba shi ne ma’anar fadin albarkacin baki ba kamar yadda wasu suka dauka, domin kuwa fadin albarkacin baki baya nufin tozarta wani ko mahanagarsa ko akidarsa.
980530
captcha