Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, shugaban hukumar kula da ayyukan addini na kasar Afghanistan ya bayyana cewa an samar da hanyoyi na sawake ziyara ga mutanen kasar da suke bukatar zuwa ziyara a wurare masu tsarki da suke cikin kasashen musulmi musamman Saudiyya Iran da kuma Iraki.
Rahotanni daga kasar Afghanistan sun habarta cewa, akalla mutane 9 sun rasa rayukansu sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai yau a kundundumar Harat da ke yammacin kasar.
Kakakin majlaisar gundumar Harat Muhyiddin Nuri ya ya sheda cewa, wani dan kunar bakin wake da ya shakare wata mota da bama-bamai kuma ya tarwatsa kansa a cikin mutane, inda ya kasha jami'an tsaro uku da kuma fararen hula 6, ya ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka rasa rayukansu ya karu, bisa la'akari da mutanen da suke cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.
Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai a garin Harat a cikin 'yan shekarun nan, wanda hakan ya sanya ake lissafa gundumar harat a matsayin yanki mai zaman lafiya a kasar Afghanistan.
981399