Bangaren kasa da kasa, al’ummar kasar Bahrain za su gudanar da tarukan makon shahada da zai hada da zanga-zanga da kuma gangami a dukaknin yankunan kasar domin neman hakkokinsu da aka haramta musu da kuma nuna goyon bayansu ga Abdulhadi Al-khawajah tsohon shugaban kungiayr kare hakkin bil a dama na kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, al’ummar kasar Bahrain za su gudanar da tarukan makon shahada da zai hada da zanga-zanga da kuma gangami a dukaknin yankunan kasar domin neman hakkokinsu da aka haramta musu da kuma nuna goyon bayansu ga Abdulhadi Al-khawajah tsohon shugaban kungiayr kare hakkin bil a dama na kasar wanda yanzu haka mahukuntan kasar suke tsare da shia gidan kaso.
Lauya mai kare mai fafutukar kare hakkin 'yan adam da ke tsare a kurkukun Bahrain Abdulhadi Khawajah, ya nuna shakkunsa matuka kan makomar rayuwar wanda yake karewa, Muhammad Alhabashi ya bayyana cewa tun ranar Asabar da ta gabata ce suka yi magana da Abdulhadi Khawajah, tsohon shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Bahrain da aka yanke ma hukuncin daurin raid a rai, wanda yake cikin mawuyacin hali na rashin lafiya a hannun jami'an tsaro, kuma daga ranar ba su kara samun wani bayani kansa ba.
A nasa bangaren babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya kirayi mahukuntan kasar Bahrain da su bayar da dama fitar da Abdulhadi Khawajah zuwa kasar Danmark domin yi masa magani, yayin da al'ummar kasar suke ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman hakkokinsu, tare da yin kira da a gaggauta sakin Al-khawajah.
982356