Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lermf cewa, babban kungiyar mabiya addinin muslunci a kasar faransa ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da kai farmaki kan masallaci da wasu masu neman fitina da kin muslunci a kasar suka yi a garin Ajaxio da nufin haifar da fitina tsakanin mabiya addibnin muslunci da kiristanci.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kungiyar ta nuna matukar damuwa dangane da yadda masu neman fitina suke aikata irin wadannan ayyuka da suka yi daidai da ta’addanci, kuma yin hakan zai bayar da dama ga masu son ganin rashin zaman lafiya tsakanin addini ya karu, ta yadda za su fake da hakan domin cin zarafin musulmi.
Wannan babban kungiyar mabiya addinin muslunci a kasar faransa ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da kai farmaki kan masallaci da wasu masu neman fitina da kin muslunci a kasar suka yi a garin Ajaxio, ta jadda cewa za ta bi dukaknin hanyoyi da dokar kasar ta yarje domin tabbatar da cewa shari’a ta yi aikinta kan wadanda suka aikata wannan ta’addanci.
982504