Bangaren siyasa da zamantakewa, a karon farko an daga tutar kasar Afghanistan acikin yankin palastinu a tawagar goyon bayan Qods da ake gudanarwa wadda daruruwan musulmi da ma wadanda ba musulmi ba suke gudanarwa daga kasashen duniya da dama.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa a karon farko an daga tutar kasar Afghanistan acikin yankin palastinu a tawagar goyon bayan Qods da ake gudanarwa wadda daruruwan musulmi da ma wadanda ba musulmi ba suke gudanarwa daga kasashen duniya da dama da suka hada har da na larabawa da na musulmi da kasashen yammacin turai da Asia mai nisa.
Tawagar ta hada da malaman addinin musulunci malaman jami’oi da kuma masana, gami da lauyoyi da kuma masu fafutulkar kare hakkin bil adama na kasashen duniya da ma ‘yan siyasa, da nufin tabbatar wa duniya cewa batun palastinu da masallacin Qods na cikin zukatan dukaknin al’ummar musulmi.
A karon farko an daga tutar kasar Afghanistan acikin yankin palastinu a tawagar goyon bayan Qods da ake gudanarwa wadda daruruwan musulmi da ma wadanda ba musulmi ba suke gudanarwa daga kasashen duniya da dama, wanda hakan ke tabbatar da cewa duniya ta gaji da ganmin ta’addancin haramtacciyar klasar Isra’ila kan al’ummar palastinu.
982535