IQNA

Za A Gudanar Da Wani Zaman Taro Kasar India Kan Fadakar Musulmi

Bangaren fikira da ilimi, za a gudanar da wani zaman taro a kasar India wanda zai yi dubi kan matsayin fadakar msuulmi da larabawa acikin wannan shekara da kuma abubuwan da suka biyo baya boren wasu daga cikin al’ummomin larabawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro a kasar India wanda zai yi dubi kan matsayin fadakar msuulmi da larabawa acikin wannan shekara da kuma abubuwan da suka biyo baya boren wasu daga cikin al’ummomin larabawa wanda ya yi sanadiyar faduwar wasu daga cikin shugabannin mulkin kama karya na larabawa.
A bangare guda kuma wani rahoton ya yi nuni da cewa adadin masallatai ya karu da kashi 74 cikin dari a kasar Amurka kamar dai yadda wani rahoto ya nuna wanda kungiyar jama’at Iman ta watsa a yau da ke cewa wannan adadi ya karu ne a cikin shekaru goma da suka gabata har zuwa karshen shekara ta 2011.
A cikin shekara ta 2000 masallatan da suke fadin kasar amurka a cikin dukkanin jahohi hamsin na kasar adadin bai wuce 1209 ba, amma ya zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha daya adadin ya karu kashi saba’in da hudu idan aka kwatanta da wancan adadin, in da ya kai masallatai 2106 a cikin jahohi hamsin na kasar.
A cikin wani bangare na wannan rahoto an yi ishara da cewa, mafi yawan matasa mabiya addinin muslunci mazauna kasar Amurka, sun yi amannar cewa manyan jami’an gwamnatin kasar suna tsananin gaba da addinin muslunci da koyarwarsa, amma hakan ba zai hana su ci gaba da gudanar da harkokinsu na muslunci ba.
A cikin irin wannan yanayi day adaga cikin majalisar shura ta musulmin Amurka ya ce duk da matsin lamabar baya-bayan nan, an karbi mabiya addinin muslunci a cikin al’ummar Amurka duk kuwa da cewa su ne marassa rinjaye.
982794