Bangaren kasa da kasa, Hassan yakub dan majalisar dokokin kasar Lebanon ya bayyana cewa wasu bayanai daga suka samu daga kasar Libya suna nuni da cewa Imam Musa Sadr tare da abokan tafiyarsa su biyu har yanzu suna raye.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na lebanese Forces cewa, Hassan yakub dan majalisar dokokin kasar Lebanon ya bayyana cewa wasu bayanai daga suka samu daga kasar Libya suna nuni da cewa Imam Musa Sadr tare da abokan tafiyarsa su biyu har yanzu suna raye a wani wuri a cikin kasar ta Libya.
Imam Musa Sadr dai ya yi tafiya zuwa kasar Libya ne bayan da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar kanar gaddafi ya aike masa da goron gayyata, inda daga bisani ya sace su kuma tun daga lokacin ba a kara jin duriyarsu ba har inda yau take, amma bayanin da aka samu na nuni da cewa akwai gagarumin ci gaba kan makomar tasu.
Dan majalisar dokokin na kasar Lebanon ya bayyana cewa bayanai da suka samu daga kasar Libya suna nuni da cewa Imam Musa Sadr tare da abokan tafiyarsa su biyu har yanzu suna raye ne a wani wuri da Gaddafi ya boye su, kuma a cewarsa da sannu bayanin zai bayyana.
983290