IQNA

Binciken Makomar Imam Musa Sadre

14:34 - April 14, 2012
Lambar Labari: 2304363
Bangaren kasa da kasa:Adnan Mansur ya karyata wasu labarai da wasu kafafen watsa labarai na yankin da kuma na kasashen larabawa na samun gawar imam Musa Sadre da cewa har yanzu suna kan bincike kuma bincike zai ci gaba.





Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Adnan Mansur ya karyata wasu labarai da wasu kafafen watsa labarai na yankin da kuma na kasashen larabawa na samun gawar imam Musa Sadre da cewa har yanzu suna kan bincike kuma bincike zai ci gaba. An nakalto daga majiyar jaridar Al'akhbar ta kasar Labanon cewa: adnan Mansur ministan harkokin wajen kasar ta Labanon na nuni da wasu labarai da kafafen watsa labarai na cikin gida da kuma na kasashen larabawa a yankin ke yadada na samin gangar jikin Imam Musa Sadre da cewa wannan labara karya ne kuma ya yi nisa da gaskiya .A ranar ashirin da hudu ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne a wata tattaunawa ta musamman da yayi da jaridar Al'akhaabar dangane da labarin da ake yadawa na samin gangar jikin wannan bawon Allah da shekaru da dama babu labarinsa da komarsa bayan day a ziyarci kasar Libiya a lokacin mulki kuma karkashin gayyatar shugaban kasar ta Libiya Mu'ammar Kaddafi da cewa muma kamar kowa haka muke jin labarin samin gawar Imam Musa Sadre kuma wannan labara babu kamshin gaskiya a cikinsa.Labarin na cewa an samu gawar imam Musa Adre a a makabartar yankin Tajura'a a kasar libiya kuma ana gudanar da binciken DNA a asibici a halin yanci.

984493
captcha