Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: al'ummar kasar Masar a jiya juma'a ashirin da biyar ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya suka gudanar da gagaramar zanga-zanga ta yin Allah wadai da takarar neman shugabancin wannan kasa da Umar suleyman na hannun damar habararran shugaban kasar ta Masar kuma dank am karya Husni Mubarar da cewa wani yunkuri ne na neman canja akalar juyin da al'ummar kasar suka yi.A Dabra da haka shima
Shugaban kungiyar malaman Musulunci ta duniya Sheikh Yusuf Qaradawi ya zargi wasu mamabobin majalisar mulkin sojan Masar da cewa suna biyayya ga raayoyin hambararren shugaba mai kama karya Husni Mubarak.
Rahoton Ikhwan Online da aka watsa a yanar gizo ya nakalto cewa shehun malamin a ya yi maraba da matakin da majalisar dokokin Masar ta dauka na kafa dokar haramta wa mutane da suka rike wasu mukamai a hambararriyar gwamnati tsayawa takara.
Sheikh Yusuf Qaradawi ya kuma yi suka kan sanar da aniyar tsayawa takarar zaben shugaban kasar da Umar Sukeiman da Ahmed Shafik tsofaffin jamiaan gwamnatin Mubarak suka yi.
A jiya ne dai majalisar dokokin kasar Masar ta fitar da sabuwar dokar ta haramta wa tsofaffin jamian gwamnatin Mubarak din tsayawa takara wacce kuma suka ce zata kare juyin juya halin da alummar kasar Masar suka yi, amma dokar ba zata yi aiki ba sai majalisar mulkin soja ta amince da ita.
984499