IQNA

Majalisar Dokokin Masar Ba Ta Amince Da Takarar Mukarraban Husni Mubarak Ba

19:18 - April 14, 2012
Lambar Labari: 2304556
Bangaren kasa da kasa, majalisar dokokin kasar Masar ba ta amince da takarar mukarraban tsohon shugaban kasar Husni Mubarak ba kasantuwarsu abokan barnarsa wadanda suka keta hurumin al’ummar kasar tare da bayyana Umar Sulaiman a matsayin wanda ya fi kowa kusanci da shi.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, majalisar dokokin kasar Masar ba ta amince da takarar mukarraban tsohon shugaban kasar Husni Mubarak ba kasantuwarsu abokan barnarsa wadanda suka keta hurumin al’ummar kasar tare da bayyana Umar Sulaiman a matsayin wanda ya fi kowa kusanci da shi a lokacin da yake mulki, saboda haka ba su amince da takararsa ba.
A nasa bangaren malamin gwamnatin kasar Qatar kuma dan asalin kasar Masar Yusuf Qardawi, ya zargi wasu mamabobin majalisar mulkin sojan Masar da cewa suna biyayya ga raayoyin hambararren shugaba mai kama karya Husni Mubarak, rahoton Ikhwan Online da aka watsa a yanar gizo ya nakalto cewa shehun malamin a ya yi maraba da matakin da majalisar dokokin Masar ta dauka na kafa dokar haramta wa mutane da suka rike wasu mukamai a hambararriyar gwamnati tsayawa takara.
Yusuf Qaradawi ya kuma yi suka kan sanar da aniyar tsayawa takarar zaben shugaban kasar da Umar Sukeiman da Ahmed Shafik tsofaffin jamiaan gwamnatin Mubarak suka yi, a jiya ne dai majalisar dokokin kasar Masar ta fitar da sabuwar dokar ta haramta wa tsofaffin jamian gwamnatin Mubarak din tsayawa takara wacce kuma suka ce zata kare juyin juya halin da alummar kasar Masar suka yi, amma dokar ba zata yi aiki ba sai majalisar mulkin soja ta amince da ita.
984634

captcha