Bangaren siyasa da zamantakewa: Shekh Abdul Aziz bin Isma'il ta fito fili ya bayyana cewa; karfi da daukaka da kuma rashin mika wuya ga bukatun ma'abuta girman kai da danniya da jamhuriyar musulunci tai ran ta nuna da tsayin daka wani kalubale ne da musulmin duniya suka yi way an mamaye da danniya na duniya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Shekh Abdul Aziz bin Isma'il ta fito fili ya bayyana cewa; karfi da daukaka da kuma rashin mika wuya ga bukatun ma'abuta girman kai da danniya da jamhuriyar musulunci tai ran ta nuna da tsayin daka wani kalubale ne da musulmin duniya suka yi way an mamaye da danniya na duniya. A ranar ashirin da daya ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wata ganawa da Mustapha Najariyan Zade mai kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar Tailand da yayi da sheikh Abdul Aziz Bin Isma'il ya bayyana haka tare da fatar sauran kasashen duniya ma za su yi koyi da bin sahun da hanyar da jamhuriyar musulunci ta Iran ta rike na yin tsayin daga da kare hakkokinta da na sauran kasashen musulmi da musulmi a duniya da kuma hatta wasu kasashen da ake dannewa a duniya .har iya ya jaddada cewa wannan wani matsayi da daukaka ce mai girma ga Iran da al'ummarta da kuma sauran kasashe.
984906