Bangaren kasa da kasa:labarin da aka bayyana na saye da sayar da giya da abubuwan maye a ofisoshin jakadancin kasar Koweiti a kasashen waje ya jawo kace nace day a kai majalisar kasar wato majalisar umma ta kafa komitin bincike kan wannan lamari.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: da aka bayyana na saye da sayar da giya da abubuwan maye a ofisoshin jakadancin kasar Koweiti a kasashen waje ya jawo kace nace day a kai majalisar kasar wato majalisar umma ta kafa komitin bincike kan wannan lamari. Muslim Albarak daya daga cikin yan majalisar Umma ta kasar ta Koweiti ya shaidawa Sabah Khalid Alsabah ministan harkokin wajan kasar ta Koweiti tare da jaddada masa cewa ya bas hi makonni biyu kacal zai gabatar masa da shaidu da takardu da ke tabbatar da cin hanci da rashawa da ake tabbakawa a ofisoshin kasar a ketare idan kuma bai gabatar ba majalisar ta dauna da dakatar da binciken da aka fara kan wannan Magana. Albarak ya bayyanawa Muhammad haif daya daga cikin yan majalisar dokokin kasar mai ra'ayin addini cewa; ma'aikatar harkokin wajan kasar ta koweiti ta bawa ofisoshin jakadancin wasu kasashe masu fama da talauci damar shigowa da giya a cikin kasar ta koweiti domin samin damar biyan ma'aiakta da cike gurbin matsalar tattalin arziki da suke fuskanta.wannan lamari da wanann labara a kasar ta Koweiti ya haddasa kace n ace mai zurfi a ciki da wajan kasar.
984925