Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatolalh Isa Kasim ya bayyana cewa kafofin yada labaran kasar suna juya hakikanin gaskiyar abin da yake faruwa ta fuskacin boren jama'ar kasar masu neman hakkokinsu na 'yan kasa da aka haramta musu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Intiqad ta kasar Lebanon cewa, babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatolalh Isa Kasim ya bayyana cewa kafofin yada labaran kasar suna juya hakikanin gaskiyar abin da yake faruwa ta fuskacin boren jama'ar kasar masu neman hakkokinsu na 'yan kasa da aka haramta musu tsawon shekaru.
Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar juma'a, inda ya tabbatar da cewa al'ummar kasar Bahrain tun da suka fara borensu na zaman lafiya da lumana ne, kuma har inda yau take ba su canja daga kan hakan ba, duk kuwa da kokarin da msarautar kasar take na son kawar da hankulan mutane ta hanyar kirkirar wasu abubuwa marassa tushe.
Babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatolalh Isa Kasim ya bayyana cewa kafofin yada labaran kasar suna juya hakikanin gaskiyar abin da yake faruwa ta fuskacin boren jama'ar kasar masu neman hakkokinsu na 'yan kasa da aka haramta musu a matsayinsu na 'yan kasa.
985127