Daga cikin 'yan takaran da aka soke sunayen na su sun hada da Umar Suleman, mataimakin tsohon shugaban mulkin kama karya ta kasar Hosni Mubarak sannan kuma shugaban hukumar leken asirinsa, Khairat Shater, dan takaran da 'yan kungiyar Ikhwan al-Muslimin, Hazim Saleh Abu Ismail dan takaran 'yan salafiyya na kasar da kuma Aiman Nur jagoran jam'iyyar al-Ghad.
Hukumar zaben kasar, cikin sanarwar soke sunayen 'yan takaran da ta fitar, ta bayyana cewar sakamakon rasa cika wasu sharuddan da kundin tsarin mulkin kasar ya shata a matsayin dalilan daukan wannan matsayar. Wadannan sharudda kuwa sun hada batun daure dan takaran Ikhwan din da aka yi a baya wanda doka ta hana shi damar tsayawa, shi kuwa dan takaran 'yan salafiyya an soke sunan nasa ne saboda kasantuwar mahaifiyarsa Ba'amurkiya ce, shi kuwa Umar Sulaiman saboda kusacinsa da tsohuwar gwamnatin Mubarak. To baya ga dukkanin wadannan abubuwan, babban abin da ya fi jan hankalin shi ne cewa wasu daga cikin 'yan takaran da aka haramta wa tsayawa din mutane ne da suke da jama'a da zai ba su damar lashe zaben. Musamman dan takaran 'yan kungiyar Ikhwan wanda ita ce jam'iyyar da ta lashe zaben 'yan majalisar kasar da aka gudanar don haka ake ganin yana da dukkanin damar zama shugaban kasar duk kuwa da kokarin da wasu suke yi na ganin hakan ba ta faru ba watakila hakan ne ma ya sanya 'yan Ikhwan din sanar da sunan Muhammad Marsi a matsayin wani dan takaran nasu na daban matukar dai aka hana shi babban dan takaran nasu tsayawa kamar yadda a halin yanzu ta faru.
A bangare guda kasashen yammaci da wasu na larabawa sun yi iyakacin kokarinsu wajen ganin Umar Sulaiman ya zama shugaban kasar wanda ko shakka babu tamkar gwamnatin Mubarak ce ta dawo, to amma a halin yanzu da aka yi waje da shi, wasu rahotanni suna nuni da cewa wadannan kasashen suna ta kai gwauro su kai mari wajen ganin sun juya zaben zuwa ga tafarkin da zai tabbatar musu da manufofinsu da hana masu kishin addini damar lashe zaben. Hakan ne ma ya sanya wasu tunanin cewa daga dukkan alamu za su koma ne ga Amru Musa, tsohon babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa, da goya masa baya wajen samun wannan matsayi wanda suke ganin hakan a matsayin abin da ya fiye musu a kan masu kishin Musulunci su lashe zaben.
Ko ma dai mene ne, abin da babu shakka cikinsa shi ne cewa wannan zaben na Masar zabe ne mai muhimmancin gaske ga bangarori daban-daban na kasashen waje don kuwa tunani da mahanga ta siyasa ta shugaban kasar Masar na farko bayan kifar da gwamnatin kama-karya ta Hosni Mubarak wanda kuma ita ce za ta shata irin matsayar da kasar Masar din za ta dauka kan lamurra daban-daban lamari ne mai muhimmancin gaske sannan kuma mai tasiri cikin lamurran cikin gida da waje na wadannan kasashe musamman wadanda suke makwabtaka da Masar din. Ko shakka babu Amurka da sauran kawayenta na yankin nan da ma na duniya za su so samun wani shugaban kasa a Masar wanda zai zamanto kamar Mubarak wanda ba abin da ya sa a gaba in banda kare musu manufofinsu da kuma tabbatar da tsaron HKI.
To amma daga dukkan alamu da wuya su sami hakan musamman idan aka yi la'akari da irin zanga-zangar da mutanen kasar suka fara don nuna rashin amincewarsu da irin wannan kokarin musamman bayan sanar da takarar Umar Suleman wanda suke ganin hakan a matsayin hatsari ga nasarar da juyin nasu ya samu.
986040