IQNA

Isra’ila Ta Haramtawa Kiristocin Masar Shiga Birnin Qods Mai Alfarma

23:33 - April 16, 2012
Lambar Labari: 2306292
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramtawa kiristocin kasar Masar shiga zuwa ziyara abirnin Qods mai alfarma saboda canjin siyasar da aka samu a kasar Masar a cikin wannan lokaci bayan hambarar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar wanda ya ke dasawa da yahudawa da Amurka gami da gwamnatin wahabiyawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Afreek news cewa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramtawa kiristocin kasar Masar shiga zuwa ziyara abirnin Qods mai alfarma saboda canjin siyasar da aka samu a kasar Masar a cikin wannan lokaci bayan hambarar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar wanda ya ke dasawa da yahudawa da Amurka gami da gwamnatin wahabiyawan saudiyya.
Wani labarin kuma daga Masar ya yi nuni da cewa, karon farko za a fitar da jaridar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa wadda kuma za ta fara fito nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa jagoran jam’iyyar Gadir ta kasar Masar kumababban sakataren majalisar koli ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar masar Muhammad Duraini shi ne ya bijiro da batun bude wannan jaridar, kuma zai bayar da gagarumar gudunmawarsa domin ci gabanta.
Wannan dai shi ne karon farko da za a fitar da wata jarida ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa a kasar ta Masar.
986048



captcha