IQNA

Limaman Masallatan Juma’a Na Fadin Kasar Masar Sun Gudanar Da Zama

23:33 - April 16, 2012
Lambar Labari: 2306295
Bangaren kasa da kasa, limaman masallatan juma’a na kasar Masar sun gudanar da babban zamansu domin tattauna muhimamn batutuwa da suke da alaka da ayyukansu ta yadda za su kara himma wajen mayar da hankali ga wayar da kan jama’a kan koyawar addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, limaman masallatan juma’a na kasar Masar sun gudanar da babban zamansu domin tattauna muhimamn batutuwa da suke da alaka da ayyukansu ta yadda za su kara himma wajen mayar da hankali ga wayar da kan jama’a kan koyawar addinin muslunci musamman a cikin wannan lokaci da kasar take cikin rudani.
A wani rahoton kuma, wahabiyawan kasar Masar sun kawafa wani kwamiti na umurni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna wanda da dama daga cikin al’ummar kasar suka yi Allawadai da shi kamar yadda ita ma jami’ar Azhar kan kafa wannan kwamiti domin aiwatar da manufar wata kasa da ke bin akidar wahabiyanci da ke yankin.
Al’ummar kasar Masar dai suna zargin gwamnatin kasar saudiyya da hannu kai tsaye wajen taimaka wa ‘yan salafiyya da ke bin akidar wahabiyanci, kuma abin da yake faruwa yanzu haka a kasar ya tabbatar da wannan aniya ta wahabiyawan.
Jama’ar wahabiyawan kasar Masar sun kawafa wani kwamiti na umurni da kyakkyawa da kuma hani daga mummuna wanda da dama daga cikin al’ummar kasar suka yi Allawadai da shi kamar yadda ita ma jami’ar Azhar kan wannan batu.
985337




captcha