Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Tunisia ta yi kakakusar suka tare da yin Allawadai da kai hari da wasu masu tsatsauran ra'ayi suka yi kan wasu wuraren addini na mabiya wasu dariku a kasar, tare da bayyana cewa wannan yayi hannun riga da abin da aka yi juyi a kansa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na businessnews cewa, a cikin wani bayani da ta fitar ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Tunisia ta yi kakakusar suka tare da yin Allawadai da kai hari da wasu masu tsatsauran ra'ayi suka yi kan wasu wuraren addini na mabiya wasu dariku a kasar, tare da bayyana cewa wannan yayi hannun riga da abin da aka yi juyi a kansa a kasar a shekarar da ta gabata.
Banin ya ce wasu daga cikin masu son kawo fitina da rarrabar kanu tsakanin mabiya addinin muslunci ne suke aikata irin wadannan ayyuka, wadanda ba su da wata laka da addinin muluni a cikin abin da suike yi, domin kuwa ko a kwanakin baya sun keta alfarmar kur'ani mai tsarki, tare da bayyana hakan a matsayin 'yan bayyana ra'ayi ko fadar albarkacin baki, lamarin da ya jawo fushin al'ummar kasar.
Ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Tunisia ta yi kakakusar suka tare da yin Allawadai da kai hari da wasu masu tsatsauran ra'ayi suka yi kan wasu wuraren addini na mabiya wasu dariku a kasar, tare da bayyana cewa wannan yayi hannun riga da abin da aka yi juyi a kansa, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya akasar.
986687