Bangaren siyasa da zamantakewa, shugaban cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi a jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa kasar a shirye take ta kara fadada harkokin da suka danganci al'adu da kasar Iraki tare da yin aiki kafada da kafada a wannan bangare.
Kmafanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa cewa, shugaban cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi a jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa kasar a shirye take ta kara fadada harkokin da suka danganci al'adu da kasar Iraki tare da yin aiki kafada da kafada a wannan bangare tsakanin kasashen biyu masu makwaftaka da juna.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin tawagar jami'an kasar Iraki da suka kawo wata ziyara a kasar Iran, domin ganawa da jami'an kasar kan alaka da ke tsakanin kasashen biyu masu tsohon tarihi, wadanda suka taka gagarumar ta fuskar ilimi da yada al'adu a tarhin Musulunci.
Shugaban cibiyar bunkasa harkokin al'adu da ilimi a jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa kasar a shirye take ta kara fadada harkokin da suka danganci al'adu da kasar Iraki tare da yin aiki kafada da kafada a wannan bangare, kasantuwar suna da gagarumar rawar da suka taka kuma suke takawa awannan zamani ta wannan fuska.
986796