Bangaren fikira da ilimi, ana shirin gudanar da wani zaman taro a mataki na kasa da kasa na masu nazari da bincike kan ilmomin kur’ani mai tsarki a birnin Azamgareh na kasar India wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen duniya musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro a mataki na kasa da kasa na masu nazari da bincike kan ilmomin kur’ani mai tsarki a birnin Azamgareh na kasar India wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen duniya musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi da kuma wasu daga cikin kasashen Asia.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taron shi ne irinsa na farko da za a gudanar a matsayi na kasa da kasa akasar India, wanda kuma manyan masana daga cikin mamalan jami’oi da na addini ne kasar suka suka bukaci hakan, domin kuwa zai taimaka matuka wajen bayar da dama ga masu bincike na kasar India su samu makama da masaniya kan hakikanin ilmimin kur’ani mai tsarki.
Gudanar da wannan zaman taro a mataki na kasa da kasa na masu nazari da bincike kan ilmomin kur’ani mai tsarki a birnin Azamgareh na kasar India wanda ake sa ran zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen duniya musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi, babban sako ne ga sauran kasashe da ba na musulmi ba, da su shiga cikin yunkurin samar da fahimta ta bai daya tsaknain al’ummomin duniya.
987173