Bangaren kasa da aksa; shugaban majalisar shawara ta musulunci a lokacin ganawarsa da babban darektan komitin bayan da agaji na cibiyar agaji ta Imam Khomeini ® a kasar Labanon ya bayyana cewa: Jamhuriyar musulunci ta Iran za ta ci gaba da taimakawa kasashen labanon ,Palasdinu da suriya babu kasawa kuma ko ana ha maza ha mata.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shugaban majalisar shawara ta musulunci a lokacin ganawarsa da babban darektan komitin bayan da agaji na cibiyar agaji ta Imam Khomeini ® a kasar Labanon ya bayyana cewa: Jamhuriyar musulunci ta Iran za ta ci gaba da taimakawa kasashen labanon ,Palasdinu da suriya babu kasawa kuma ko ana ha maza ha mata.An nakalto wasu majiyoyin kusa da majalisar shawarar musulunci ta Iran cewa; Muhamamd Barjawi babban darektan komitin bayar da agaji da kula da agajin a cibiyar bayar da agajin na Imam Khomeini ® a kasar Labanon kuma tsohon wakilin kungiyar Hizbullahi a majalisar kasar a lokacin wata gabata ce da yayi da shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Ali Larjani a ranar ashirin da ashirin da tara ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya tabbatar masa da cewa jamhuriyar musulunci ta Iran za ta ci gaba da taimakawa al'ummomi da kasashen labanon ,Palasdinu da kuma Suriya kuam ya jinnawa kokarin da himmar babban sakataren kungiyar Hizbullahi Hasan Nasrullahi da wadanda suka yi shahada na kungiyar musamman shahid Imad Mugniya wanda ya raya himmar wannan kungiyar a yan shekarun baya bayan nan musamman a lokacin yakin kwanaki talatin da uku daka kallawa kungiyar da al'ummar Labanon kuma a yakin dab a a taba ganin irinsa ba domin ya gilgiza da cin nasara kan gwamnatin danniya da kama karya ta yahudawan sahayoniya ma'abuta girman kai a duniya da kuma masu mara masu baya.
988924