Bangaren kasa da kasa, Imam musa Sadr ya kasance a sahun gaba a kowane lokaci wajen koyar da haramtacciyar kasar Isra'ila darasi a duk lokacin da ta yi shishigi kan al'ummar kasar Lebanon wanda kuma kokarinsa ne ya haifar da gwagwarmayar al'ummar Lebanon a halin yanzu da take gasawa yahudawa aya a hannu.
Kamanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lebanonfiles cewa, Imam musa Sadr ya kasance a sahun gaba a kowane lokaci wajen koyar da haramtacciyar kasar Isra'ila darasi a duk lokacin da ta yi shishigi kan al'ummar kasar Lebanon wanda kuma kokarinsa ne ya haifar da gwagwarmayar al'ummar Lebanon a halin yanzu da take gasawa yahudawa aya a hannu kamar yadda duk duniya ta gani a cikin shekarun nan.
Khalil Hamdan mamba a kungiyar Amal ya bayyana cewa, a koda yaushe Imam musa sadr ya kasance mai matukar bukatar ganin musulmi sun fahimci hadarin haramtacciyar kasar Isar'ila, tare da hankoron ganin ya fadakar da su hanyoyin da za su fuskanci barazanar yahudawan sahyuniya, wanda rashin yin hakan tabbas zai jefa al'umma ckin mawuyacin hali.
Imam musa Sadr ya kasance a sahun gaba a kowane lokaci wajen koyar da haramtacciyar kasar Isra'ila darasi a duk lokacin da ta yi shishigi kan al'ummar kasar Lebanon wanda kuma kokarinsa ne ya haifar da gwagwarmayar al'ummar Lebanon a halin yanzu da take gasawa yahudawa aya a hannu, kamar ta kasance a yakin kwanki talatin da uku.
987723