IQNA

Kungiyoyin Musulmi na Sukan Ziyarar Muftin Masar A HKI

17:33 - April 21, 2012
Lambar Labari: 2309309
Bangaren kasa da kasa: wasu daga cikin kungiyoyin musulmi da wasu fitattun musulmi a kasar Masar a ranar laraba talatin ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya sun yi Allah wadai da tofin Allah tsine kan ziyarar da Ali Jum'a muftin kasar Masar ya kai ziyara a yankin kudus da haramtacciyar kasar Isra'ila suka mamaye.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wasu daga cikin kungiyoyin musulmi da wasu fitattun musulmi a kasar Masar a ranar laraba talatin ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya sun yi Allah wadai da tofin Allah tsine kan ziyarar da Ali Jum'a muftin kasar Masar ya kai ziyara a yankin kudus da haramtacciyar kasar Isra'ila suka mamaye. An nakalto daga majiyar CPI cewa: hadin guiwar cibiyar bincike da ke karkashin jami'ar Azhar ta kasar masar a ranar alhamis talatin da daya ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya ta gudanar da taron gaggauwa karkashin shugabancin Ahmad Aldaib shugaban jami'ar ta Azhar domin yin bincike da nazarin ziyarar da muftin kasar ta Masar ya kai yankin kudus da ziyaratar masallacin kudus a daidai wannan lokaci da birnin ke karkashin mamaye da wuce gonad a irin gwamnatin zalunci da mamaye ta haramtacciyar kasar Isra'ila . Mahalarta wannan taron sun yi mamaki matuka gaya da jin wannan ziyara ta muftin na kasar masar da kuma yadda ya zabi wannan lokaci na kai ziyararsa a wannan yanki na Palasdinu da ke karkashin mamayen gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila kuma musamman a wannan loaci da ake samin sauye sauye da canje canjen gwamnatoci da ke zama yan amshin shatan manyan kasashen duniya.
989578
captcha