IQNA

Kafafen Yada Labarai Na Da rawar Da Za Su Taka Domin Warware Matsalar Palastine

22:31 - April 22, 2012
Lambar Labari: 2310220
Bangaren kasa da kasa, kafofin yada labarai na kasashen musulmi na da gagarumar rawar da za su iya takawa domin warware matasalar ad al’ummar palastinu suke ciki ta hanyar bayyana hakikanin abin da ke faruwa na zaluncin haramtacciyar kasar Isra’ila akansu ga mtanen duniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar The Sun Daily cewa, kafofin yada labarai na kasashen musulmi na da gagarumar rawar da za su iya takawa domin warware matasalar ad al’ummar palastinu suke ciki ta hanyar bayyana hakikanin abin da ke faruwa na zaluncin haramtacciyar kasar Isra’ila a kansu ga mtanen duniya, musamman ma ganin cewa sauran kasashen yammacin suna kokarin boye hakika.
Wannan magana ta zo ne daga bakin babban jami’i mai kula da bangaren yda labarai na kungiyar hadin kan kasashen musulmi a wani zaman taro da kungiyar ta gudanar a kasar Gabon kan ayyukan kafofin yada labarai dangane da abubuwan da suke faruwa a duniyar musulmi, musamman kan alummar palastinu marassa kariya.
Issam Sati ya ce kafofin yada labarai na kasashen musulmi na da gagarumar rawar da za su iya takawa domin warware matasalar ad al’ummar palastinu suke ciki ta hanyar bayyana hakikanin abin da ke faruwa na zaluncin haramtacciyar kasar Isra’ila a kansu ga mtanen duniya wadanda suka jahilci hakikanin abin da ke faruwa.
988973

captcha