IQNA

An Yi Allawadai Da Kisan Kiyashin Da Masarautar Bahrain Take Kan Fararen Hula

22:34 - April 22, 2012
Lambar Labari: 2310224
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taro na kungiyoyin kare hakkin bil adam ana kasa da daka a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon inda bayanin bayan taron ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da mahukuntan kasar Bahrain kan matakan rashin imani da suke dauka kan fararen hula masu zanga-zangar lumana a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanart gizo na grt.gov cewa, an gudanar da wani taro na kungiyoyin kare hakkin bil adam ana kasa da daka a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon inda bayanin bayan taron ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da mahukuntan kasar Bahrain kan matakan rashin imani da suke dauka kan fararen hula masu zanga-zangar lumana a kasar musannan a cikin lokutan nan.
Mahukunta a kasar Bahrain sun sako 'yar mai rajin kare hakkokin bil'adama na kasar Abdulhadi al-Khawaja, wato Zainab al-Khawaja daga gidan yari bayan da kama ta da kuma ci gaba da tsare ta na kwanaki da jami'an tsaro suka yi.
Lauyan Zainab al-Khawajan ne ya sanar da hakan inda ya ce jami'an tsaron sun sako ta bayan kwanaki suna tsare da ita sakamakon shiga cikin zanga-zangar da al'ummar kasar suka shirya don a saki mahaifinta wanda mahukunta suka yanke masa hukumcin daurin rai da rai sakamakon shirya zanga-zangar neman sauyi a kasar da mahukunta suka ce wani kokari ne na kifar da gwamnatin kasar.
Yayin da ya ke magana kan yanayin da Abdulhadi al-Khawajan, wanda yake ci gaba da yajin cin abin na tsawon watanni biyu, Lauyan yace yana cikin mawuyacin hali ainun. 'Yan adawa a kasar Bahrain din dai sun ja kunnen mahukuntan da su guji abin da zai biyo baya matukar dai al-Khawajan ya rasu sakamakon yajin cin abincin da suke yi.
989928

captcha