IQNA

Taron Addini Kan Zagayowar Ranar Shahadar Fatima Zahra (AS) A Nasiriya.

Bangaren kasa da kasa: mu'assisar Iamain Alkazimiyain (AS) a yankin Nasiriya na kasar Irakiza su gudanar da taron addini na shekara shekara ta suke gudanarwa a dalilin zagayowar irin wannan rana ta diyar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shit a yi shahada Fatimatul Zahra (AS) kuma a ranar bakwai ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a gudanar da wannan taro.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musuluncin ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mu'assisar Iamain Alkazimiyain (AS) a yankin Nasiriya na kasar Irakiza su gudanar da taron addini na shekara shekara ta suke gudanarwa a dalilin zagayowar irin wannan rana ta diyar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shit a yi shahada Fatimatul Zahra (AS) kuma a ranar bakwai ga watan Urdebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a gudanar da wannan taro.Jama’a masu saurare barkanmu da saduwa da ku a wannan shiri na musamman da zamu gabatar muku domin ranar Arba’in wato cikan kwanaki arba’in da shahadar Imam Husaini {a.s} wanda ake kiran wannan ranar da yaumul-Arba’in. Yaumul-Arba’in rana ce da iyalan gidan Manzon Allah {s.a.w} suka sake dawowa filin Karbala domin ziyara da gudanar da alhini da juyayin kisan gillar da aka yi wa shugaban samarin gidan aljanna Imam Husaini da iyalan gidansa da sahabbansa. Amma kafin fara shirin namu, a madadin ma’aikatan sashen hausa na muryar Jamhuriyar musulunci ta Iran muna taya dukkanin al'ummar musulmi alhini da juyayin wannan rana, tare da rokon All… Madaukaki da ya isar wa iyalan gidan Manzonsa kan bakin zaluncin da suka fuskanta daga al'umma a bayan shugaban talikai.

Dalilan Gwagwarmayar Imam Husaini {a.s}.

A shirin namu zamu yi kokarin bijiro wasu daga cikin dalilan da suka sanya Imam Husaini {a.s} daukan matakin gudanar da gwagwarmaya ne da ta kai shi ga sadaukar da ransa da na iyalan gidansa gami da na zababbun sahabbansa domin Allah.

Imam Husaini dan Ali dan Abi-Talib {a.s} a matsayinsa na jagoran shiriya da Allah ya daura masa alhakin shiryar da al'umma zuwa ga hanya madaidaiciya a zamaninsa; akwai hakkokin addini da dama da sun hau kansa, kuma wadannan hakkoki sun wajabta masa daukan matakin gudanar da gwagwarmaya domin sauke su, wanda a sakamakon haka ya samu babban rabo na shahada.

Hakika Imam Husaini {a.s} ya gabatar da huduba ga rundunar Hurr dan Yazid Arriyahi da ta fara killace shi a kan hanyarsa ta zuwa Kufah, inda a cikin hudubar Imam Husaini {a.s} ke fayyace muhimman dalilan da suka wajabta masa yunkurin gudanar da gwagwarmaya koda kuwa zai kai ga shahada.

A cikin hudubar Imam Husaini {a.s} yana bayyana cewa:-
"Ya ku mutane, hakika Manzon Allah {s.a.w} ya ce; duk wanda ya ga azzalumin shugaba, mai halatta abin da Allah ya haramta, mai karya alkawarin Allah, mai sabawa sunnar Manzon Allah, yana gudanar da zalunci da ayyukan laifi a tsakanin bayin Allah, mutum bai tashi domin kawar da shi a aikace ko da baki ba, to hakkin Allah ne ya shigar da shi mashigar wannan azzalumin shugaban. Ku saurara hakika wadannan mutane {Bani-Umayya} sun rungumi biyayya wa shaidan, sun kaurace wa biyayyan Allah mai rahama, sun fito fili suna bayyana fasadi da barna, sun jinginar da dokokin Allah gefe guda, sun wawushe dukiyar baitul-mali, sun halatta abin da Allah ya haramta, sun haramta abin da Allah ya halatta, don haka ni ne na fi cancantar tashi domin kawar da wannan zalunci".

A cikin wannan huduba ta Imam Husaini {a.s} zamu fahimci darussa kamar haka:-

{1} Matsayin jagoranci da shiryarwa:- Imam Husaini {a.s} a matsayinsa na jagoran shiriya a tsakanin al’umma kuma hujjan Allah a bayan kasa, lalle wajabcin gudanar da gwagwarmaya domin kare addinin Musulunci daga rushewa ya hau kansa.

Hakika mahukuntan Bani Umayya sun yi kokarin shafe hasken addinin Musulunci da kawar da shi daga kan doron kasa, sakamakon adawarsu da addinin Musulunci da manzon Allah da ya zo da sakon Musulunci. Babban dalili kan haka shi ne furucin da ya fito daga shugaban daular Bani Umayya a wannan zamanin Yazidu dan Mu'awiya da ke bayyana kafircinsa da bijirewarsa ga addinin Musulunci a fili a mashahurin furucinsa da ke cewa:

" لَعِبتْ هاشمُ بِالمُلك فَلا خَبَرٌ جاءَ وَلا وَحْيٌ نَزَلْ "
"Hakika Bani Hashim sun yi wasa da mulki saboda babu wani sako ko wahayi da ya sauko musu".

Hakika wannan furuci na Yazidu dan Mu'awiya yana fayyace akidarsa ce ta jahiliyya da take cikin zuciyarsa, wadda ke tabbatar da rashin imaninsa da sakon wahayi da aka saukar ga manzon Allah, don haka bai yi imani da alkur'ani da aljanna da kuma wuta ba a matsayinsa na shugaban daular Musulunci a wannan lokacin.

{2} Hakkin kare addinin Musulunci daga gurbata:- Hakika wajabcin kare addinin Musulunci da martabarsa da kuma tabbacin ganin ya ci gaba da wanzuwa a bayan kasa a matsayin karshen sakon addini daga wajen Allah, ya hukunta wa Imam Husaini {a.s} mikewa domin kalubalantar tsarin mulkin zalunci na mahukuntan Bani Umayya da suke gurbata addini ta hanyar halatta mummunan aiki da Allah ya haramta da kuma haramta kyakkyawan aiki da Allah ya halatta, da kuma karya alkawarin Allah da sabawa sunnan manzon Allah {s.a.w} da bayyana fasikanci a fili a matsayin shugabannin addini.

{3} Hakkin kare tsarin zamantakewar al'umma:- Hakika matsayin Imam Husaini {a.s} na jagoran shiriya a tsakanin al'umma, hakkin kare rayuwar al'ummar da na dukiyoyinsu ya hau kansa wanda hakan ya wajabta masa gudanar da gwagwarmaya domin kare rayuka da dukiyoyi al’umma daga ayyukan zaluncin mahukuntan Bani Umayya koda kuwa hakan zai kai shi ga sadaukar da rayuwarsa mai albarka. Don haka Imam Husaini {a.s} ya mike ya gudanar da gwagwarmaya domin dawo da adalcin Musulunci da tsarin rayuwar mai aminci a tsakanin al'umma.

{4} Kafa hujja ga al'ummar da suka bayyana shirinsu na sadaukar da kai domin kawar da zalunci a bayan kasa:- Hakika Imam Husaini {a.s} ya kafa hujja a kan al'umma ta hanyar shelanta jihadi a kan azzaluman shugabanni da nufin 'yantar da al'umma daga kangin zalunci da barna. Lalle mutanen Kufa na kasar Iraki sun aike da sakonnin wasiku ga Imam Husaini {a.s} suna neman da ya zame musu jagora domin 'yantar da su daga tsarin mulkin kama karya na Bani Umayya, tare da daura masa alhakin mummunan halin da suka shiga matukar bai dauki matakin 'yantar da su daga kangin zaluncin Bani Umayya ba.

{5} Kare matsayin khalifanci:- Yana daga cikin dalilan gwagwarmayar Imam Husaini {a.s} tsarkake matsayin khalifancin addinin Musulunci daga daudar mahukuntan Bani Umayya da suka karbi ragamar khalifanci bada hakki ba. Hakika Bani Umayya sun gurbata matsayin khalifancin Musulunci, inda suka juyar da akalarsa zuwa ga son ransu, wanda matsayin khalifanci a wannan lokacin ya yi hannun riga da koyarwan Musulunci da ke neman wanzar da adalci da daidaito a tsakanin al'umma.

Hakika Imam Husaini {a.s} ya ga yadda Bani Umayya suka mai da khalifancin kakansa manzon Allah {s.a.w} ya zame tushen watsa barna da fasadi a bayan kasa, inda har ta kai ga khalifa a wannan lokaci yana bayyana fasikanci ta hanyar shan giya da sharholiya, don haka ya mike domin dawo da matsayi da martabar khalifancin kakansa manzon Allah {s.a.w}.

{6} 'Yantar da al'umma daga kangin mutuwar zuciya da sallamawa zalunci:- Hakika a lokacin mulkin Mu'awiya da na dansa Yazidu zuciyar al'ummar musulmi ta riga ta mutu, wadda ta rasa ruhin bijire wa zalunci, kuma mahukunta a wannan lokacin sun yi nasarar katange al'umma daga samun hasken shiriya da wayewa da zasu zaburar da su ga neman hakkokinsu, don haka al'umma suka mika kai ga tsarin danniya.

Hakika Imam Husaini {a.s} ya fadakar da al'umma matsayin jihadi, tare da zaburar da su ga sadaukar da kai domin 'yantar da kansu daga kangin zalunci da barna zuwa ga 'yanci da daukakar zuciya. Tabbas shahadar Imam Husaini {a.s} ta yi sanadiyyar haifar da gagarumin canji a tsawo tarihin Musulunci da rayuwar musulmi.
{7} Farfado da tsarin tattalin arzikin al'umma da ya durkushe:- Hakika yana daga cikin dalilan yunkurin Imam Husaini {a.s} 'yanto al'umma daga kangin talauci da rayuwar kunci da suka shiga ciki a tsarin zamantakewarsu ta yau da kullum sakamakon mummunar siyasar mahukuntan Bani Umayya ta yin sama da fadi da dukiyar al'umma.

Mahukuntan Bani Umayya sun wawushe dukiyar al'umma da ke baitul-Malin musulmi. Hakika Mu'awuya dan Abi-Sufyan ya shelanta a gaban al'ummar musulmi cewa; Lalle dukiya, dukiya ce ta Allah, ba ta musulmi ba, don haka shi yafi cancantarta. Don haka Imam Husaini {a.s} ya gudanar da gwagwarmaya domin 'yanto mutane daga babakeren mahukuntan Bani Umayya a kan dukiyar al'umma.

{8} 'Yantar da al'umma daga kangin Zalunci:- Hakika zalunci da cin zali sun lullube rayuwar al'umma a dukkanin kasashen musulmi, inda mahukunta ke sarrafa rayuwar mutane yadda suka ga dama ta hanyar zubar da jinin duk wani mahaluki. Don haka gwagwarmayar Imam Husaini {a.s} ta zaburar da al'umma da bude musu hanyar jihadi domin kubutar da kansu daga kangin zaluncin mahukunta.

{9} Yaki da bakar siyasar mahukuntan Bani Umayya ta shafe duk wata alamar Musulunci da abubuwa masu kima da ke cikin addinin Musulunci:- Hakika mahukuntan Bani Umayya sun dauki matakin shafe duk wata alama ta Musulunci da rusa abubuwa masu kima da ke cikinsa, inda suka yi kokarin shafe matsayin iyalan gidan manzon Allah wato Ahlul-Baiti {a.s}.

Malaman tarihi da na hadisai sun habarto irin rawar da Mu'awuya dan Abu-Sufyan ya taka a fagen rusa matsayin iyalan gidan manzon Allah da kur’ani ya wajabta yi musu salati ta hanyar sunnanta zaginsu da la'antarsu a kan mumbarin masallatai, kuma haka aka ci gaba da horar da al'ummar musulmi a dukkanin sassa ta duniya a tsawon shekaru.

Hakika gwagwarmayar Imam Husaini {a.s} ta fadakar da al'ummar musulmi babban hatsarin da addinin Musulunci da musulmi suka afka ciki, hatsarin da ya kai ga fara kashe 'ya'yan manzon Allah bayan zaginsu da la'antarsu a tsakanin musulmi.

{10} Kare hakkinsa na khalifanci:- Hakika yana daga cikin dalilan yunkurin Imam Husaini {a.s} kare hakkinsa na khalifanci da mahukuntan Bani Umayya suka kwace ba a kan hakki ba. Tabbas a karkashin yarjejeniyar da aka cimma ta sulhu tsakanin Imam Hasan Al-Mujtaba {a.s} da mu'awiya dan Abu-Sufyan sun tsaida sharadin cewa: Imam Husaini {a.s} ne zai kasance khalifa a bayan Mu'awiya, don haka Imam Husaini {a.s} ne halattaccen khalifa a zamanin ba Yazidu dan Mu'awiya ba.

{11} Umurni da kyakkyawan aiki da hani da mummunan aiki:- Hakika yana daga cikin manyan dalilan da suka wajabta wa Imam Husaini {a.s} gudanar da gwagwarmaya da sadaukar da rayuwarsa mai daraja, umurni da kyakkyawan aiki da hani da mummunan aiki, saboda sune ginshikan addinin Musulunci, kuma Imam Husaini {a.s} ne ya fi cancantar daukan wannan babban matsayi na addini.

Hakika Imam Husaini {a.s} ya yi furuci da wannan matsayi na shi a cikin sakon wasiyar da ya gabatar ga dan uwansa Muhammad Bin Hanafiyya, a lokacin da zai fice domin sadaukar da ransa mai albarka da cewa: "Hakika Ni ban yi wannan fita domin girman kai ko domin alfahari ba, kuma ba fita ba ce domin zalunci ko barna ba, iyaka dai fita ce da na yi domin neman gyara a al'ummar kakana, kuma ina nufin yin umurni ne da kyakkyawan aiki da hani da mummuna".

{12} Kawar da bidi'a da ta watsu a tsakanin al'umma:- Hakika mahukuntan Bani Umayya sun dauki matakin watsa bidi'a da gangan a tsakanin al'ummar musulmi da nufin shafe hakikanin koyarwan addinin Musulunci da rusa shi.

Imam Husaini {a.s} ya yi nuni da wannan lamari a cikin sakon wasikarsa da ya aike da shi ga mutanen garin Basra da cewa: "Lalle an shafe sunna, kuma an rayar da bidi'a". Sakamakon haka Imam Husaini {a.s} ya mike domin kawo karshen bidi'ar jahiliyya da Bani Umayya suke watsawa a cikin al'ummar musulmi, da shimfida hakikanin koyarwan sakon addinin Musulunci da kakansa manzon Allah {s.a.w} ya zo da shi.

{13} 'Yantar da kai daga kangin kaskanci:- Yana daga cikin dalilan yunkurin Imam Husaini {a.s} 'yantar da kansa daga kangin kaskanci da mutuwar zuciya. Hakika mahukuntan Bani Umayya sun yi nufin tursasawa Imam Husaini {a.s} mika kai ga manufofinsu cikin kaskanci, amma sai ya yi watsi da wannan bukata, inda ya gwammace ya sadaukar da rayuwarsa cikin 'yanci da daukaka, kamar yadda ke bayyana hakan a cikin jawabansa a ranar ashura da cewa: "Lalle kaskantacce maras asali dan maras asali ya shimfida mini hanya dayan biyu tsakanin yaki da kaskanci, to Allah ya nisantar da mu daga kaskanci, kuma Allah da manzonsa suna ki mana wannan kaskanci, kuma zuciya tana kyamatarsa, sannan dabi'a ta daukakar zuciya tana kin mika wuya ga yin biyayya ga kaskantacce a kan mutuwar daukaka".
Tarihin Ranar Arba’in Wato Yaumul-Arba’in.

Cikan kwanaki arba’in da shahadar Imam Husaini {a.s} da iyalan gidansa da sahabbansa ya zo ne daidai da ranar 20 ga watan Safar shekara ta 61 bayan hijira, wato rana mai kamar ta yau.

Ziyarar Jabir a ranar arba’in.

Jabir dan Abdullahi Ansari {r.a} ya kasance daga cikin manyan sahabban Manzon Allah {s.a.w}, kuma shi ne farkon wanda ya ziyarci kabarin Imam Husaini {a.s} bayan cikan kwanaki arba’in da shahadarsa {a.s}.

Bawan Jabir da ake kira Ada عطا yana cewa; Na kasance tare da Jabir dan Abdullahi Ansari a ranar ashirin ga watan Safar, yayin da muka isa Ghadiriyya, Jabir ya tsaya ya yi wanka, ya sanya tufarsa mai kyau, sannan ya ce mini; shin akwi turare tare da kai; Ya kai Atah? Sai na ce masa akwai turare, bayan ya shafe kansa da sauran jikinsa, sannan sai ya kama hanya ba tare da takalma a kafafunsa ba, har ya kai ga wajen kabarin Imam Husaini {a.s}, sannan ya tsaya a wajen kan Imam Husaini {a.s} ya yi kabbara sau uku, sai Jabir ya fadi sumamme, bayan ya farfado sai na ji yana sallama ga ma’abuta kabari …

A lokacin da Jabir dan Abdullahi Ansari da bawansa Adah da sauran mutane suke ci gaba da gudanar da ziyara ga Imam Husaini {a.s} a wannan rana ta arba’in, sai suka hango wata tawaga ta tunkaro su daga hanyar Sham, sai Jabir ya ce wa bawansa; je ka ka zo mana da labari dangane da wannan tawaga, idan rundunar Umar dan Sa’ad ne da suka kashe Imam Husaini {a.s} sai mu tsere mu nemi mafaka, idan kuma Ali dan Husain Zainul-Abidin {a.s} ne, to na ‘yanta ka domin Allah.

Bayan bawan nan ya tunkari tawagar, ba a jima ba sai gashi ya dawo da labari yana cewa; Ya Jabir mike ka tarbi zuriyar manzon Allah {s.a.w}, wannan tawaga ta Imam Ali Zainul-Abidin {a.s} ne da ke tafe da iyalan gidansa. Sai Jabir ya mike ya tunkari tawagar babu takalma a kafafunsa, kuma babu rawani a kansa, bayan ya kusato tawagar, sai Imam Ali Zainul-Abidin {a.s} ya ce masa; Shin wannan Jabir ne? Sai Jabir ya amsa da cewa; kwarai ni ne; Ya dan manzon Allah, sai Imam Ali Zainul-Abidin {a.s} ya ce; Ya Jabir a nan ne wallahi aka kashe mazajenmu, aka yanka yaranmu, aka kame matanmu a matsayin fursunonin yaki, kuma aka kona tantunanmu.

Hakika tawagar Imam Ali Zainul-Abidin {a.s} ta iso Karbala ne a ranar ashirin ga watan Safar wato bayan cikan kwanaki arba’in da shahadar Imam Husaini {a.s}, inda tawagar ta gudanar da ziyarar kabarin Imam Husaini {a.s} da na iyalan gidansa da sahabbansa, kuma suka gudanar da zaman juyayi da alhini na tsawon kwanaki a wannan wajen.

Hakika an ruwaito hadisai daga jagororin shiriya na iyalan gidan manzon Allah da suke kwadaitar da muminai kan ziyarar kabarin Imam Husaini {a.s}.

Har ila yau, koyi da iyalan gidan Imam Husaini {a.s} da suka taso daga kasar Sham zuwa Iraki domin zirarar kabarin Imam Husaini {a.s} da kuma hadisai da aka ruwaito daga jagororin shiriya na iyalan gidan manzon Allah, al’ummar musulmi musamman ‘yan shia daga kowane bangare na duniya sun kasance suna ziyarar kabarin Imam Husaini {a.s} a kowace shekara a rana arba’in ga watan Safar domin neman lada daga Allah Madaukaki.


991797