Bangaren nazari da ilimi: a wani zaman addini da masana da kuma manazarta hadi da shugabannin addini a Jamus a taron ad suka bawa taken abubuwan day a hada addinin musulunci da addinin Kiristanci a yankin gabas ta tsakiya kuma a jiya hudu ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a zauran cibiyara tuntubar juna da fahimtar addini da wayewa a hukumar da ke kula da al'adu da dangantaka irin ta musulunci aka gudanar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musuluncin ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a wani zaman addini da masana da kuma manazarta hadi da shugabannin addini a Jamus a taron ad suka bawa taken abubuwan day a hada addinin musulunci da addinin Kiristanci a yankin gabas ta tsakiya kuma a jiya hudu ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a zauran cibiyara tuntubar juna da fahimtar addini da wayewa a hukumar da ke kula da al'adu da dangantaka irin ta musulunci aka gudanar. Da Dama daga cikin mahalarta wannan taron sun bada shawara da cewa duk wani rikici da sabanin fahimta a tsakanin mabiya wadannan addinai na musulunci da kiristanci za a iya warwarewa ta hanyar fahimta da kuma zama kan tebirin tattaunawa kuma idan aka yi la'akari da abubuwan day a hada mabiya addinan guda biyu za a iya fahimtar cewa abubuwa masu muhimmanci ne ya hada su da kuma za su iya taimakawa yankin na gabas ta tsakiya wajan samin zaman lafiya da ci gaba ta dukan bangarori kama daga bangaren addini ne ko na siyasa da zamantakewa ,al'adu da tattalin arziki da tsaro da dai sauransu.
991835