IQNA

Fim Din Yusuf Ta Samu Karbuwa Mai Girma A Kasar Senegal

Bangaren al'adu da fasaha; Aliyon Ciyon shugaban gidan radiyo da talbijin na Lamp Falla a kasar Senegal a wata ganawa ce da yayi da mai kula da ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Senegal ya bayyana cewa; fim din tarihi ta annabi Yusuf (AS) ta samu gagaramin karbuwa a tsakanin al'ummar kasar ta Senegal.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musuluncin ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Aliyon Ciyon shugaban gidan radiyo da talbijin na Lamp Falla a kasar Senegal a wata ganawa ce da yayi da mai kula da ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Senegal ya bayyana cewa; fim din tarihi ta annabi Yusuf (AS) ta samu gagaramin karbuwa a tsakanin al'ummar kasar ta Senegal. Shi ma mai kula da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar ta Senegal ya jinjina da yabawa wannan gidan talbijin kan jan aiki da yake gudanarwa da yadda ta samu karbuwa a tsakanin al'ummomin wannan kasa karkashin jan aiki da yadda kuma take gudanar da aikinta cikin tsari da gaskiya da kuma babban abu mai muhimmanci a kokarinta na fadakar da jama'a. wannan gidan talbijin a kasar ta Senegal na taka rawar gani da samin karbuwa a tsakanin matasan kasar kuma a aranar ashirin da takwas ga watan Oktoban shekara ta dubu biyu das ha daya ne ta fara gudanar da ayyukanta da suka shafi addinin musulunci a cikin harshen kasar na Senegal Walf da kuma Faransanci.
991819